Janar Faruk Yahaya ya Umarci Sojojin Najeriya da su Kai Yaƙi Zuwa Maboyar ‘Yan Ta’adda da ‘Yan fashi

 

Babban hafsan sojojin kasa (COAS), Laftana-Janar Faruk Yahaya, ya kammala rangadin kwanaki biyu na sansanin sojoji a jahar Katsina.

Kwamandan sojojin ya yi alkawarin cewa sojoji za su kawar da ‘yan ta’adda da ke addabar mazauna yankin arewa.

Yahaya ya ce ana kokarin shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi a kasar a yanzu.

Daura, jahar Katsina – Babban hafsan Sojojin kasa (COAS), Faruk Yahaya, ya umarci sojojin Najeriya da su kai yaƙi zuwa maboyar ‘yan ta’adda da’ yan fashi.

Kwamandan rundunar ya bayar da umarnin a ranar Juma’a, 7 ga watan Agusta, lokacin da yake yi wa sojoji jawabi a sansanin Fort Muhammadu Buhari dake Daura, jahar Katsina.

Yahaya ya bayyana cewa duk da cewar akwai ƙalubale, amma yakamata sojoji su ƙuduri aniyar cin nasarar yaƙin, The Sun ta ruwaito.

Yace:

“Wannan shine abin da muke yi kuma wannan shine abin da za mu ci gaba da yi. Domin duk wurin da na wuce, sakona kenan. Dole ne mu kai yaƙin zuwa wuraren abokan gaba a nan arewa maso yamma har ma a arewa maso gabas inda muke gudanar da su.”

A cewar Jaridar This Day, Yahaya wanda shi ma ya kai ziyarar ban girma ga Sarkin Daura Umar Farouk Umar, ya nemi goyon bayan sarakunan gargajiya a arewa maso yamma don samun ingantattun bayanai da za su taimaka wa sojoji wajen yakar annobar ta’addanci.

Ya ce wannan muhimmiyar rawa ce da ƙananan hukumomin za su taka kuma yana da mahimmanci wajen yaƙi da ayyukan masu laifi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here