Yaki da Rashin Gaskiya Nauyi ne da Bai Kamata a Bar wa Jami’an Hukumar EFCC Kadai ba – Abdulrasheed Bawa

 

Abdulrasheed Bawa ya ce EFCC za ta bi doka muddin yana shugaban hukumar.

Bawa ya ce zai ajiye mukaminsa da zarar an bukaci ya yi abin da ya saba doka.

A shekarar nan ne aka nada Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC Shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ya yi magana game da abin da zai sa shi ya bar kujerar da yake.

Daily Trust ta rahoto cewa Mista Abdulrasheed Bawa ya sha alwashin yin murabus daga shugaban EFCC idan aka bukaci ya yi abin daa ya saba doka.

Da aka yi hira da Abdulrasheed Bawa a wani shiri a gidan talabijin na NTA na kasa, ya bayyana cewa zai bi doka wajen duk aikin da zai yi a kujerarsa ta EFCC.

Bawa ya ce yaki da rashin gaskiya nauyi ne da bai kamata a bar wa jami’an hukumar EFCC kadai ba.

Sabon shugaban na hukumar ya yi kira ga al’umma su daina ganin darajar bata-gari da mutane marasa gaskiya da su ka samu arziki ta hanyoyin da ba su dace ba.

“Mu na bukatar mu canza dabi’armu a Najeriya. Mun saba da bauta wa wadanda mutanen da su ke da dukiya a al’umma, amma ba mu tambayar silar arzikinsu.” Mista Bawa yake cewa: “Wajen cin nasara a yaki da rashin gaskiya, mu na hada-kai da duk masu ruwa da tsaki, kamar jagororin addinai, shugabanni da dai sauransu.”

“Za mu shiga wayar da kai domin a jawo hankalin mutane su kaurace wa duk wata hanyar rashin gaskiya.” “Zan cigaba da yin abin da ya ke daidai.

A karkashina, hukumar EFCC za ta cigaba da yin biyayya ga dokar kasa. Duk wanda ya tambaye ni in yi abin da nake jin ba daidai ba, ko ya saba wa doka, zan yi murabus, in ajiye aiki na.”

Kun samu rahoto cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ya kafa hukumar EFCC a shekarar 2003 domin yaki da rashin gaskiya da masu damfarar jama’a.

Daga lokacin da aka kafa hukumar, Nuhu Ribadu, Farida Waziri, Ibrahim Lamorde, Ibrahim Magu, da Mohammed Abba duk sun rike ta kafin zuwan Abdulrasheed Bawa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here