Wannan Yakin Zai Kasance na Tsawon Lokaci, Sakamakon Kuma Zai Kasance Mai Yawa – Ministan Tsaron Isra’ila
Yayin da sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya sake komawa Isra’ila a ranar Litinin din nan, babban jami’in diflomasiyyar na Amurka na ganawa da jerin manyan jami’an gwamnatin kasar, bayan rangadin da ya kai kasashen Gabas ta Tsakiya.
Read Also:
Da yake jawabi kafin Anthony Blinken, ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya shaida masa cewa “wannan zai kasance yaki na tsawon lokaci, sakamakon kuma zai kasance mai yawa, amma mu ne za mu yi nasara – don kasar Isra’ila da al’ummar Yahudawa da kuma akidojin da duka kasashenmu biyu suka yarda da su”.
Ya yaba wa Amurka saboda goyon bayan da take bai wa Isra’ila kuma ya ambaci jiragen ruwan dakon jiragen yakin Amurka biyu da ta tura zuwa gabashin Tekun Bahar Rum tun bayan harin da Hamas ta kai wa Isra’ila.