‘Yan Boko da Masu Fada Aji Sune Matsalar Najeriya – Sarkin Musulmai
Sarkin musulmi ya bayyana cewa, ‘yan boko su ne matsalar Najeriya a halin da ake ciki.
Ya bayyana haka ne a jahar Gombe yayin wani taron da ya gudana na addinai a jahar ta Gombe.
Ya kuma kalubalanci shugabanni da cewa su koma ga littafan addininsu domin samun mafita.
Gombe – Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana cewa ’yan boko da masu fada aji a kasar nan sune matsalar Najeriya.
Read Also:
Alhaji Sa’ad Abubakar ya fadi hakan ne a yayin wani taron wanzar da zaman lafiya da gina kasa da Kwamitin Shirya Da’awah na Kasa ya shirya karo na uku a Jahar Gombe.
Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa, a yayin taron ne kwamitin wanda ya hada mabiya addinin Kirista da Musulmi ya tattauna matsalolin da ke hana ruwa gudu wajen samun zaman lafiya a kasar nan.
A jawabinsa, Sarkin Musulmi ya kalubalanci shugabannin da cewa su koma wa littatafan su masu tsarki don samun ginshikin shugabanci na gari.
A cewarsa, muddin aka rasa kyakkyawan shugabanci to za a rasa zaman lafiya da hakan zai tarwatsa duk wani hadin kai a tsakanin al’umma.
A farko tun kafin taron ne Sarkin Musulmin ya jagoranci bude wata hanya a garin Gombe da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya gina kuma aka sanya mata sunansa a Unguwar Gandu da ke bayan gidan Sarkin Gombe.