‘Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe ‘Yar Majalisar Kasar Somaliya

 

Akalla mutum 15, ciki har da wata ‘yar majalisar kasar Somaliya sun halaka, bayan da wasu ‘yan kunar bakin wake suka kai hare-hare biyu a garin Beledweyn na tsakiyar kasar.

Firaminista Mohamed Hussein Roble ya bayyana kashe Amina Mohamed Abdi a matsayin “kisan gilla”. Shi kuma shugaban kasar Abdullahi Farmajo ya aika da sakonsa na ta’aziyyar ta Twitter:

Cikin mamatan akwai tsohon dan majalisa Hassan Dhuhul da wasu sojojin Somaliya.

Kafofin yada labarai a yankin na cewa yawan mamatan na iya zarce alkaluman wadanda aka sanar a yanzu.

Babbar tashar talabijin ta Somaliya ta wallafa wasu hotuna na wadanda aka kashe yayin harin.

Kungiyar Al-Shabab ta dauki alhakin kai hare-haren – wadanda aka kai a biranen Mogadishu da tsakiyar Beledweyne.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here