‘Yan Ta’addan Boko Haram Sun Kashe Malaman Makaranta Uku a Yobe

 

An kashe malaman makaranta uku a jahar Yobe makon da ya gabata.

Wannan ya auku ne lokacin da yan Boko Haram suka kai hari Geidam.

Mutan garin Geidam sun gudu daga muhallansu bayan harin da yan ta’addan suka kai.

Yan ta’addan Boko Haram da suka kai hari karamar hukumar Geidam, a jahar Yobe, makon da ya gabata sun hallaka akalla Malaman makaranta uku.

A cewar Daily Trust, an kashe biyu cikin Malaman a makarantar Government Technical School, Geidam, yayinda aka kashe daya a gida.

Yan ta’adda sun yi kokarin jan hankulan matasa domin su shiga tafiyarsu. Sun bankawa gidajen ma’aikatan gwamnati da yan siyasa wuta bayan kwashe kayayyakin alfanu.

Mutan garin sun bayyana cewa ba zasu taba manta abubuwan da suka faru cikin kwanaki biyar da yan Boko Haram suka kwace garin ba.

Hakazalika, yan ta’addan sun rabawa mazauna garin Geidam a jahar Yobe kudi domin shigar da su cikin harkar ta’addancin da suke yi.

HumAngle ta samu rahoton cewa yan ta’addan sun yi rabon N20,000 ga kowane gida ga gidaje akalla 50 da yammacin Talata.

Yan ta’addan sun kai hari karamar hukumar ne da yammacin Juma’a, 23 ga Afrilu, kuma suka kwace garin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here