Mafi Yawancin ‘Yan Bindiga da ke Adabar mu Fulani ne – Gwamna Masari
Gwamna Aminu Masari ya ce mafi yawancin ‘yan bindigan da ke arewa maso yamma Fulani ne.
Gwamnan na jahar Katsina ya kuma ce ‘yan bindigan da ke yankin arewa galibinsu musulmai ke kamar shi.
Gwamna Masari ya ce ‘yan arewa da dama ba za su yarda da abin da ya fada ba amma zancensa gaskiya ne.
Jahar Katsina – Gwamna Aminu Masari na jahar Katsina ya ce mafi yawancin ‘yan bindiga fulani ne kaman shi, ya kara da cewa suna magana harshen Fulfulde kuma suna cewa su musulmai ne, The Punch ta rawaito.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana a shirin siyasa na ‘Politics Today’ a gidan talabijin na Channels.
Read Also:
Kalamansa:
“Mutane ne kaman ni, wadanda ke magana da harshe irin nawa, kuma su na cewa suna addini irin nawa.
“Don haka abin da muke fama da shi shine ‘yan bindiga; ba baki bane daga wani duniyan, mutane ne da suke zama da mu na daruruwan shekaru.
“Masu shigowa daga kasashen Afirka ta Yamma da Afirka ta Arewa suma Fulani ne.
“Mafi yawancin ‘yan bindiga da ke adabar mu Fulani ne, ko da yana da dadin ji ko ba shi da dadin ji amma dai wannan shine gaskiya.
Ba cewa na ke yi dukkan Fulani ne ba amma galibinsu fulani ne, kuma wadannan mutane ne da ke zaune a daji kuma babban sana’arsu shine kiwon dabobi.”
Ya kara da cewa akwai kimanin kungiyoyi 100 da suka hada da ‘yan fashin daji, masu garkuwa, masu fyade da masu fashi da makami.