‘Yan Bindiga 3 da Sufeton ‘Dan Sanda 1 Sun Rasa Rayukansu a Jahar Imo

 

‘Yan bindiga sun bankawa ofishin ‘yan sanda dake Orlu a jahar Imo wuta inda ya kone kurmus.

An gano cewa miyagun sun dinga wurga bama-bamai ofishin inda ‘yan sanda suka sakar musu ruwan wuta.

‘Yan sandan sun yi nasarar sheke ‘yan bindiga 3 yayin da sifetan dan sanda daya ya halaka yayin artabun .

Orlu, Imo – Miyagun ‘yan bindiga a ranar Alhamis sun kone ofishin ‘yan sanda na Orlu inda suka halaka dan sanda mai mukamin sifeta.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, an halaka uku daga cikin ‘yan bindigan bayan musayar wuta da aka yi tsakanin miyagun da ‘yan sandan.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, CSP Mike Abattam, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Juma’a.

Lamarin ya faru wurin karfe 9 da rabi na dare yayin da ‘yan bindigan masu yawa dauke da makamai suka kai farmaki kuma suka dinga jefa bama-bamai kan rufin ofishin ‘yan sanda na Orlu.

Sifetan dan sanda ya rasa ransa.

Yace muguwar wutar da ta tashi a ofishin ‘yan sandan ta shafi wasu ababen hawa dake farfajiyar caji ofis din.

Amma kuma Abattam ya ce ‘yan sandan sun yi martani ga ‘yan bindigan kuma ruwan wuta yasa ‘yan bindigan suka yi laushi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takardar ta ce: Uku daga cikin ‘yan bindigan sun sheka lahira kuma an samu bindigoginsu yayin da sauran suka tsere zuwa cikin daji da raunika.

Amma cike da jimami an rasa ran sifetan dan sanda yayin farmakin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here