Katsina: ‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa da Mutane Tare da Kashe Wasu
Masu garkuwa sun sace a ƙalla mutane 48 daga ƙauyuka daban-daban a ƙaramar hukumar Batsari a Katsina.
Ƙauyukan da ƴan bindiga suka kai harin sun hada da Garin Dodo, Bakon Zabo, Biya-ka-Kwana, Tundun Modi da Watangadiya.
Wadanda suka sace sun hada da mata, maza har ma da wasu ma’aurata da aka sace kwana ɗaya bayan aurensu.
A ƙalla mutane 48 ne ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Batsari bayan harin da suka kai a garuruwa huɗu.
Yasir Aminu, mazaunin Garin Dodo, ɗaya daga cikin garuruwan huɗu, ya ce ya yi tafiyan awa huɗu a kafa kafin ya kai Batsari bayan yan bindigan sun hari, HumAngle ta ruwaito.
Read Also:
“Sun kai hari ƙauyen mu cikin kwanaki biyu da suka gabata, sun sace fiye da mutum 30,” in ji Aminu, ya cigaba da cewa, “mafi yawancin mutane sun gudu ba mu san inda suka tafi ba. Sun saba kawo mana hari kullum sai dai wannan ya yi muni”.
Majiyar Legit.ng ta gano cewa ƴan bindigan sun saba kai hari ƙauyukan da ke wajen Batsari na tsawon watanni uku da suka gabata.
A cikin awa 48 da suka gabata, yan bindigan sun sace mutum 30 ciki har da maza da mata a Garin Dodo, yayin da sun sace mata 10 a ƙauyen Biya-Ka-Kwana a cewar majiyoyi daga ƙauyen.
“A kauyen Tudun Modi, an sace mutum uku yayinda an sace mutum biyar a ƙauyen Watangadiya,” a cewar wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa.
“Yan bindiga sun cin karen su ba babaka a garuruwan domin an bar mutanen a hannun ƴan bindigan.”
Kazalika, an sace wasu wani ango da amaryarsa a Bakon Zabo, wani ƙauye mai nisan kilomita 3 daga garin Batsari.
Yan bindigan sun sace amarya da ango kwana ɗaya bayan ɗaura aurensu,” in ji Hassan Fari, wani shaidan gani da ido.
Ya ce har yanzu yan bindigan ba su tuntubi iyalan ba don neman kuɗin fansa kuma kawo yanzu hukumomin tsaro ba su riga sun ceto su ba.