‘Yan Bindiga Sun Halaka Jami’in da Yaje Ceto Wanda Akai Garkuwa da su

 

‘Yan bindiga sun halaka dan sanda bayan ya je ceton wasu da aka yi garkuwa da su a Jigawa.

Mummunan lamarin ya auku ne kauyen Bosuwa da ke karamar hukumar Maigatari ta jihar.

‘Yan bindiga sun sace tsoho mai shekaru 70 tare da wata budurwa mai shekaru 25.

a duniya A ranar Litinin ne ‘yan bindiga suka kashe jami’in dan sandan da ke kokarin ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su a kauyen Bosuwa da ke karamar hukumar Maigatari ta jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Channels TV a ranar Talata.

Ya yi bayanin cewa, bata-garin sun sace wani Ali Dankoli mai shekaru 70 a duniya da wata Zainab Isah, wacce diya ce wurin tsohon shugaban karamar hukumar Maigatari, Isa Zakari Bosuwa.

“Yan sanda da ke Maigatari sun samu kiran gaggawa a kan cewa wasu miyagun ‘yan ta’adda dauke da miyagun makamai sun tsinkayi kauyen Bosuwa da ke Maigatari.

“Sun yi awon gaba da wani Alhaji Ali Dankoli mai shekaru 70 da wata Zainab Isah mai shekaru 25.

“A saboda hakan, ‘yan sanda sun yi gaggawa hanzartawa tare da rufe dukkan hanyoyin shige da fice a kauyen sannan suka bibiyi miyagun.

“A wannan halin ne ‘yan bindigan suka budewa ‘yan sanda wuta, lamarin da ya kawo mutuwar dan sanda daya,” ya kara da cewa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here