‘Yan Bindiga Sun Halaka Masunci a Jahar Kaduna

‘Yan bindiga sun halaka wani masunci a karamar hukumar Zangon Kataf a Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Kaduna, Mista Samuel Aruwan ya tabbatar da hakan.

Mr Aruwan ya ce an fara bincike kan kisar da nufin gano wadanda suka aikata domin su girbi abinda suka shuka ‘Yan bindiga sun kashe wani masunci, Adamu Bala, a yayin da ya tafi rafi kama kifi a tsakanin Zango da Ungwan Ruhogo a karamar hukumar Zangon Kataf na jahar Kaduna, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Mista Samuel Aruwan, ya tabbatar da harin inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin amma bai bada karin bayani ba.
Kwamishinan ya ce, “Dakarun Operation Safe Haven sun ruwaito kisa tsakanin Zango da Ungwan Ruhogo a karamar hukumar Zangon Kataf a jahar.

“A cewar rahoton, wasu mutanen da ba a sani ba sun kashe wani Adamu Bala bayan ya tafi rafi kama kifi a ranar Litinin 12 ga watan Afrilun 2021.

“An tsinci gawarsa a gabar rafi a jiya Talata 13 ga watan Afrilun shekarar 2021.

“Gwamna Nasir El-Rufai ya yi bakin samun rahoton kuma ya yi wa iyalan wanda ya rasu ta’aziyya sannan ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin ya gafarta masa.

“A halin yanzu an fara bincike a kan lamarin.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here