‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma 11 a Jihar Sokoto

 

Tsagerun yan bindiga sun kai farmaki kan manoma a yankin gabashin jihar Sokoto a ranar Asabar, 2 ga watan Yuli.

An tattaro cewa yan bindigar sun kuma hallaka manoma 11 da ke kan gudanar da ayyuka a gonakinsu.

Mummunan harin ya afku ne a yankin garin Gandi Dalike da ke karamar hukumar Rabah ta jihar.

Sokoto – Yan fashi da makami a yankin gabashin jihar Sokoto sun kaddamar da kazaman hare-hare kan manoma, jaridar The Nation ta rahoto.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kashe manoma 11 a cikin makon da ya gabata a garin Gandi Dalike da ke yankin karamar hukumar Rabah ta jihar.

Wani mazaunin yanki ya ce yan bindigar da yawansu sun farmaki kauyen a ranar Asabar, 2 ga watan Yuli.

Sakataren hakimin Gandi, Alhaji Tukur Muhammad, ya ce maharan sun isa yankin da maraicen wannan rana sannan suka kashe wasu manoma a gonakinsu.

Rahoton ya kuma kawo cewa wani jigo a Gandi, Alhaji Idris Gandi, ya ce yan bindiga sun kashe wasu manoma hudu da ke aiki a gonakinsu a Gidan Buwai da ke kauyen Gandi a kwanan nan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here