‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Biyar a Jahar Nasarawa
Wasu yan bindiga da ba’a san ko su waye ba sun kashe manoma yan kabilar Tiv guda 5 a ƙauyen Gidan Sule, jahar Nasarawa
Lamarin ya faru ne da daren ranar Laraba, inda maharan suka mamayi mutanen ƙauyen lokacin da suka kwanta bacci.
A halin yanzun an jibge jami’an yan sanda, bijilanti, mafarauta da kuma dakarun sojin ƙasa domin tabbatar da komai ya dai-daita.
Aƙalla manoman kabilar Tiv guda biyar ne wasu yan bindiga da ake zargin fulani ne suka kashe a ƙauyen Gidan Sule, karamar hukumar Keana, jahar Nasarawa.
Shugaban ƙungiyar cigaban Tiv a jahar, Kwamared Peter Ahemba, shine ya bayyana haka a wata fira da dailytrust a Lafiya, babban birnin Nasarawa.
Ahemba yace maharan sun mamaye ƙauyen, inda suka kai hari kan mutanen da daddaren ranar Laraba yayin da mutane ke bacci.
Yan bindigan sun hallaka mutum huɗu nan take yayin da ragowar ɗayan ya karisa bayan an kai shi asibiti.
Yace: “Mutum 5 muka rasa a wani harin yan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne a ƙauyen Gidan Sule ranar Laraba da daddare.”
“Huɗu daga cikin sun mutu nan take yayin da ɗayan akai tsammanin zai tashi, amma daga baya ya karisa a asibiti.”
Read Also:
“Mutanen Nasarawa masu son zaman lafiya ne. Babu wani rashin jituwa tsakanin yan kabilarmu da waɗanda ake zargin fulani makiyaya ne a yankin, shiyasa nake mamakin meye dalilin kawo mana hari.”
Ya kuma yi kira yan kabilarsa ta TIV da su kwantar da hankalinsu yayin da jami’an tsaro suke kokarin dawo da zaman lafiya a yankin.
Ƙungiyar fulani zata gudanar da bincike Da aka tuntuɓe shi ta waya, shugaban ƙungiyar fulani Miyetti Allah reshen jahar Nasarawa, Bala Dabo, yace sam ba shi da labarin an kai hari a ƙauyen.
Amma yayi alƙawarin cewa zai gudanar da bincike kan lamarin domin tabbatar da waɗanda ke da hannu a kai harin.
“Ba’a sanar dani komai game da harin ba, saboda haka ba zan iya tabbatar da mutanen mu ne suka kai harin ba.
Amma ina tabbatar muku da cewa zamu bincika don tabbatar da ainihin abinda ya faru ranar Laraba da daddare,” inji shi.
Yan sanda sun fara ɗaukar mataki Da yake tabbatar da lamarin a Lafiya, Kakakin yan sandan jahar, ASP Ramhan Nansel, yace daga sanda hukumar ta samu rahoton harin aka ɗauki matakin tura yan sanda, jami’an tsaron bijilanyi, mafarauta tare da haɗin guiwar dakarun soji zuwa yankin.
Ya yi alƙawarin cewa za’4 kamo yan bindigan dake da hannu a harin kuma a gufanar da su domin hakan ya zama izini ga sauran mutane.