‘Yan Bindiga Sun Harbi Tsohon Dan Majalisar Dokokin Jahar Sokoto

 

‘Yan bindiga sun kai wa tsohon dan majalisar dokokin jahar Sokoto, Abdulwahab Goronyo hari a gidansa.

Yayin harin, sun harbi tsohon dan majalisar a kafarsa sannan sun kuma awon gaba da matarsa.

Majiya daga iyalan tsohon dan majalisar ta tabbatar da harin da aka kai masa a cikin dare.

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kai tsohon dan majalisar dokokin jahar Sokoto, Abdulwahab Yahaya Goronyo hari sun kuma yi awon gaba da matarsa.

SaharaReporters ta gano cewa an kai wa tsohon dan majalisar hari ne a gidansa da ke karamar hukumar Goronyo a ranar Litinin.

“Yan bindiga sun kai wa Hon Abdulwahab hari a daren jiya, sun harbe shi a kafarsa sun kuma tafi da matarsa,” a cewar wani majiya daga iyalensa.

Sokoto na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma a Nigeria inda yan bindiga ke adabar mutane. Masu garkuwa da mutane da yan bindiga sun dade suna kai wa al’umma hare hare.

Gwamnatin jahar ta yi yarjejeniyar sulhu da yan bindigar a shekarar 2019. Amma duk da hakan har yanzu ana kai wa garuruwa da dama hare hare inda a wasu lokutan ake sace mutane don karbar kudin fansa ko kuma a kashe su.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here