‘Yan Bindiga Sukai Hari a Giwa, Jahar Kaduna

 

Wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari karamar hukumar Giwa, jahar Kaduna, bayan sojoji sun gama kakkabe abokansu.

Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida a Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da sake kai harin ‘yan bindigar a cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin.

A cewar Aruwan, ‘yan bindigar sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane da dama.

Yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane da dama a kauyen Garawa, karamar hukumar Giwa jahar Kaduna.

Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan da rundunar sojin sama ta samu nasarar kakkabe wasu yan bindiga a garuruwan Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun.

Kwamishinan harkokin tsaro na cikin gida, Mr Samuel Aruwan ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Aruwan ya bayyana cewa hukumar tsaro na ci gaba da bincike kan harin da aka kai Giwa, yayin da aka tsaurara matakan tsaro a yankin.

Ya ce yan bindigar sun kai hari tare da kashe mutane biyu a wurare daban daban da ke a karamar

A cewar sa, an kashe Alhaji Sa’adu a gundumar Fatika yayin da yan bindigar suka sace wasu mutane.

“Haka zalika, yan bindigar sun far wa kauyen Doka duk a cikin gundumar Fatika, inda suka yi garkuwa da wasu mutane.

“A kauyen Angwan Dan Yaya, a wannan gundumar, yan bindigar sun kashe wani mutum mai suna Alhaji Suleiman Audu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here