‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Cikin Garin Yobe

Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa ana artabu yanzu haka.

Wannan karon jahar Yobe yan ta’addan Boko Haram suka kai hari.

Wasu yan bindiga da ake zargin yan Boko Haram ne sun kai farmaki Geidam, wani gari jahar Yobe da yammacin Laraba, 6 ga watan Junairu, 2021.

Yanzu haka misalin karfe 6:30 na yamma sun kan kai harin. Harbe-harben ya tayar da hankalin mazauna garin kuma hakan ya sa suka gudu cikin daji yayinda wasu suka boye cikin gidajensu.

Jaridar Premium Times ta samu ji daga bakin wani a garin wanda ya bayyana halin da suke ciki.

“Harbe-harben da ake a waje yayi yawa. Ba zan iya magana ba yanzu,” mazaunin ya laburta.

Kakakin hukumar yan sanda jihar, Abdulkarim Dungus, ya bayyana cewa ya tuntubi DPO na yankin lokacin suna artabu da yan ta’addan.

“Na kira DPO na Geidam kuma suna artabu. Ina jin karar bindigarsa. Ya yi alkawarin kiransa,” Dungus ya bayyana.

Geidam mahaifar tsohon gwamnan jihar Yobe ne kuma Sanata mai ci yanzu, Ibrahim Geidam.

Garin na da nisam kilomita 200 da birnin jihar Damaturu kuma tana iyaka da jamhuriyyar Nijar. Wannan ba shi ne karo na farko da yan Boko Haram ke kai hari garin ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here