‘Yan Bindiga Sun Kashe Akanta a Harin da Suka Kai Cross-River
‘Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Kuros Ribas inda su ka bindige wani akanta a ma’aikatar ilimi ta jihar.
Maharan sun bi akantan ne har kusa da tsohon gidan gwamnati bayan sun biyo shi daga banki inda su ka kwace kudaden hannunshi.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Irene Ugbo ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Larabar 29 ga watan Nuwamba a Calabar.
Jihar Kuros Riba – Wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Kuros Riba inda su ka yi ajalin wani akanta.
Akantan da ke aiki a ma’aikatar ilimi ta jihar ya rasa ransa ne a yau Laraba 29 ga watan Nuwamba, Legit ta tattaro.
Yaushe maharan su ka hallaka akantan?
Read Also:
Maharan sun bi akantan har zuwa kusa da tsohon gidan gwamnatin jihar kafin su ka harbe shi a cinya.
Daily Nigerian ta tattaba cewa maharan sun biyo akantan tun daga banki inda ya je cire kudade har zuwa inda su ka yi ajalinshi.
Birinin Calabar a kwanakin nan na fama da hare-haren ‘yan bindiga musamman a kan babura.
Mene ‘yan sanda su ka ce kan harin?
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan su guda biyu sun tilasta akantan ba su jakar kudin kafin bindige shi har lahira.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Irene Ugbo ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Larabar 29 ga watan Nuwamba a Calabar.
Irene ya ce an kwashi akantan zuwa asibitin sojojin ruwa don ba shi kulawar gaggawa.
Ya kuma yi Allah wadai da harin inda ya ce jami’ansu sun bazama don zakulo wadannan mahara.