‘Yan Bindigan da Suka Sace Daliban Jami’ar Greenfield Sun Kashe Dalibai 3

 

Kwanaki uku bayan garkuwa da su, an tsinci gawawwakinsu a cikin daji.

Gwamnan jahar Kaduna ya yi Alla-wadai da wannan kisan gillan da aka yiwa dalibai.

Wannan ya biyo bayan kisan ma’aikacin jami’ar guda daya a ranar da akayi garkuwan.

Yan bindigan da suka kai hari jami’ar GreenField dake Kaduna inda sukayi awon gaba da dimbin dalibai sun bindige mutum 3 cikin daliban da suka sace.

Hakan na kunshe cikin jawabin da Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan Kaduna, Samuel Aruwan, ya saki ranar Juma’a. An tsinci gawawwakin daliban uku ranar Juma’a a kauyen Kwanan Bature, dake kusa da jami’ar, Aruwan ya kara.

“Cikin wani halin rashin tausayi da mugunta, yan bindigan da suka sace daliban jami’ar Greenfield sun bindige dalibai 3,” yace.

“An tsinci gawawwakin daliban uku yau (Juma’a) a kauyen Kwanan Bature, wani waje dake kusa da jami’ar kuma kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida da kwamandan Operation Thunder Strike, Lt.Col. MH Abdullahi sun kai gawawwakin dakin ajiye gawawwaki.”

“Gwamna El-Rufa’i ya yi Alla-wadai da kisan wadannan daliban uku kuma ya siffanta matsayin mugunta.. Ya ce yan bindiga sun zama ashrarun mutane kuma ya wajaba a yakesu bisa zaluncinsu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here