Jami’ar Greenfield: ‘Yan Bindigan da Suka Sace Daliban Sun Sake Kashe Dalibai 2

Yan bindiga masu garkuwa da mutanen da suka sace dalibai a jami’ar Greenfield dake jahar Kaduna sun sake bindige biyu cikin kimanin dalibai 22 da suka sace.

Gwamnatin jahar Kaduna ta bayyana cewa ta tsinci gawawwakin daliban ne cikin daji.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan jahar, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a jawabin da ya sake ranar Litinin.

Wannan na faruwa ne kwanaki uku bayan yan bindigan sun kashe dalibai uku cikinsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here