‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Dan Kasuwa a Sabon Gari Da ke Jihar Kano

 

Yan bindiga sun tafi har shago sun bindige wani dan kasuwa mai suna Mr Ifeanyi a Sabon Garin Jihar Kano.

Shaidun gani da ido sun bayyana yadda maharan suka taho a mota suka tsallaka titi suka nufi shagon Ifeanyi.

Maharan sun fara harbin abokin Ifeanyi sannan suka bi shi a lokacin da ya yi yunkurin tserewa suka bindige shi har lahira.

Kano – Yan bindiga sun harbe wai dan kasuwa, Mr Ifeanyi, har lahira sun kuma raunata abokinsa a wurin sana’arsa a sabon garin Zaria a Jihar Kano.

Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar a Azubros Plaza, France Road, Sabon Garin Kano.

Shaidun gani da ido sun magantu

Shaidu sun ce babu wanda ya san inda yan bindigan suka fito ba har sai da suka ji karar harbin bindiga, suka ce maharan sun bindige mutumin sannan suka tsere a motarsu.

Wani shaida wanda ya nemi a sakayya sunansa ya ce:

“Sun zo ne musamman don su kashe Ifeanyi bisa fahimtar mu. Sun tsallako daga titi suka tafi shagosa. Abokinsa suka fara harbi lokacin da Ifeanyi ya tsere daga shagonsa sai suka bi shi suka bindige shi har lahira.

“Ba su taba kowa ba kuma abin ya daure mana kai. Wurin ya hargitse. Amma bayan sun tafi, komai ya koma daidai sai dai cinkoson motocci.”

Wani shaidan gani da idon, Jibrin Usman ya ce an garzaya da abokin marigayin da aka harba zuwa asibiti yana samun sauki. Duk da cewa kawo yanzu ba a san dalilin kashe shi ba, Daily Trust ta gano cewa marigayin fitaccen dan kasuwa ne da ke sayar da batiri a kasuwan Sabon Gari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here