‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Fitaccen Mafarauci

Daya daga cikin mafarautan jihar Adamawa, Young Mori, ya riski ajalinsa a jihar Kaduna da safiyar Talata.

Kamar yadda bayanai suka kammala, masu kiwon shanu ne suka kashe shi bayan sun sha musayar wuta.

Mori yana daya daga cikin mafarautan da aka gayyato tun daga jihar Adamawa don taya yaki da ‘yan ta’adda.

An kashe shugaban kungiyar mafarauta na jihar Adamawa, Young Mori, a wata musayar wuta da suka yi da ‘yan bindiga a jihar Kaduna, kamar yadda iyalansa da wasu majiyoyi suka tabbatar.

Mori yana daya daga cikin mafarautan da aka gayyata don kokarin yaki da ‘yan ta’adda a jihohin arewa. Shugaban kungiyar, Salihu Wobkenso, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, an kashe Mori ne a Kaduna. “Wannan mummunan labari ne ga mafarautanmu. Young Mori, daya daga cikin jaruman mafarautan jihar Adamawa daga karamar hukumar Guyuk ya riski ajalinsa a jihar Kaduna. Masu kiwon shanu sun kashe shi da safiyar yau.”

Wobkenso bai bayar da wani bayani dalla-dalla ba a kan mutuwar, sai dai ya bayyana irin alhinin da jama’a suka shiga sakamakon mutuwar, Premium Times ta wallafa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here