Wani Shugaban PDP Ya Rasu Bayan ‘Yan Bindiga Sun Harbe Shi – Lawal Dako

 

Allah ya yi wa Alhaji Lawal Dako, shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Sabuwa a Katsina rasu.

Alhaji Lawal Dako ya rasu ne sakamakon harbinsa da ‘yan bindiga suka yi yayin wani hari a ranar 8 ga watan Nuwamban 2020.

Tun bayan harin, an marigayin ya dinga jinya a kuma ya rasu a Asibitin Koyarwa ta Ahmadu Bello Zaria a ranar 20 ga watan Nuwamba.

‘Yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na karamar hukumar Sabuwa a Jihar Katsina, Alhaji Lawal Dako.

A cewar Katsina Post, yan bindiga sun harbe Lawal Dako ne a ranar 8 ga watan Nuwamban shekarar 2020 amma ya rasu a ranar 20 ga watan Nuwamba sakamakon raunin da ya samu yayin harin da suka kai masa.

Marigayin ya rasu na Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga a

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here