Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Malamin Jami’a – Dr Karl Kwaghger
Jami’an tsaro sun tsinci gawar wani Malami a Jami’ar aikin gona, Makurdi.
An iske Dr. Karl Kwaghger jina-jina a hanya bayan an yanka makwogoronsa.
Zuwa yanzu babu wanda ya san wadanda su ka yi wannan danyen aiki a jihar.
Rahotanni su na bayyana mana cewa ‘yan bindiga sun hallaka wani malamin makaranta a jami’ar koyon harkar noma a Makurdi, jihar Benuwai.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa wannan lamarin ya auku ne a yankin gidauniyar J.S Tarka a cikin unguwar Makurdi da ke jihar Benuwai.
Daga baya an fahimci cewa Dr. Karl Kwaghger ne malamin da ya mutu a hannun wadannan miyagu.
Read Also:
Karl Kwaghger ya kai matsayin mataimakin farfesa a sashen fasaha a jami’ar tarayyar ta FUAM. Da nan da ‘dan lokaci kadan zai kure harkar boko.
Jaridar ta ce sai da wadannan mutane su ka fara rotsa kan Karl Kwaghger da wani abu mai matukar karfi, sannan sai aka yanka masa makwogoro.
‘Yan bindigan sun yi maza-maza sun tsere bayan sun yi wannan aika-aika, kuma rahotanni sun nuna har yanzu ba a gano wadannan mahara ba.
Shugaban kungiyar ASUU na reshen jami’ar FUAM, Dr. Ameh Ejembi, ya tabbatar wa manema labarai da mutuwar wannan abokin aikin nasa dazu.
Ita ma shugabar hulda da jama’a ta FUAM, Rosemary Waku ta fadawa Punch, babu shakka sun rasa ma’aikacinsu, amma ba ta bayyana yadda ya mutu ba.
‘Yan sanda sun dauki gawar mutumin sun adana a dakin ajiya.Za a binciki abin da ya kashe sa.” Inji Kakakin ‘yan sandan Benuwai, Catherine Anene.