‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 41 a Jahar Zamfara

‘Yan bindiga a jahar Zamfara sun halaka manoma 41 tare da sheke dan sanda daya.

Miyagun sun kai hari kauyukan Tofa da Samawa inda suka far wa manoma a gonakinsu.

An gano cewa ‘yan bindigan basu saci komai ba a kauyukan, illa iyaka kisan da suka yi.

‘Yan bindiga sun sake kashe manoma 41 a kauyukan Tofa da Samawa na karamar hukumar Bungudu ta jahar Zamfara.

Wani mazaunin yankin wanda yace sunansa Malam Balarabe, ya sanar da The PUNCH cewa ‘yan bindigan sun kutsa yankin yayin da manoman ke gonakinsu suna shuka, wasu kuma suna gyaran gona.

“Kwatsam suka bayyana sannan suka dinga harbin manoman inda suka kashe da yawa daga ciki,” Balarabe ya jaddada.

Ya kara da yin bayanin cewa ‘yan bindigan sun kara da rufe titunan da zasu sada jama’a zuwa kauyukan biyu inda suka kashe wasu manoman dake komawa gida.

Balarabe yace manoma 41 ne suka rasa rayukansu inda ya kara da cewa ‘yan bindigan basu dauka komai daga kauyukan biyu ba.

“Sun je yin kisa ne kawai kuma manoman dake gona suka je kashewa,” Balarabe ya kara da cewa.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar, Mohammed Shehu, ya ce, “Rundunar hadin guiwa ta ‘yan sandan bata san da labarin ba sai bayan ‘yan bindigan sun gama kashe-kashe a yankin Tofa.Har yanzu bamu san yawan wadanda suka kashe ba.”

“Amma kuma, yayin da ‘yan bindigar suka bar Tofa suna kan hanyar kauyen Samawa domin kai wani hari, ‘yan sandan dake kauyen Samawa sun gaggauta isa tare da musayar luguden wuta da ‘yan bindigan.

“A sakamakon arangamar, an kashe ‘yan bindigan da ba a san yawansu ba yayin da wasu suka tsere da miyagun raunika.

Ba a samu rashin rai ko daya ba a garin Samawa. Sai dai dan sanda daya ya amsa kiran Ubangijinsa,” Shehu yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here