‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 5 a Jahar kaduna

 

Wasu mahara da ake zargin yan bindiga ne sun halaka mutum 5 a karamar hukumar Chikun a Kaduna.

Wadanda aka kashe sune Samson Danladi, Luka Gajere, Amos Ali, Titus Baba da Damali Musa.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Kaduna, Mr Samuel Aruwan ne ya bada sanarwar.

Wasu yan bindiga sun kai hari kauyen Katarma da ke karamar hukumar Chikun na jahar Kaduna inda suka halaka mutane biyar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Mr Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce a ranar Lahadi maharan sun raunata mutum daya.

A cewarsa, mutum dayan da ya jikkata yana nan yana samun kulawan likitoci a wata jaha da ke makwabtaka da Kaduna.

Duk da kwamishinan bai fada lokacin da aka kai harin ba, ya bayyana wadanda suka rasu kamar haka Samson Danladi, Luka Gajere, Amos Ali, Titus Baba da Damali Musa.

“A wani labarin mai kama da wannan, Jami’an tsaro karkashin Operation Safe Haven, sun ruwaito cewa an yi fada tsakanin matasa a kauyen Atuku da ke karamar hukumar Jema’a.

Yayin fadar, wasu matasa biyu sun kaiwa wani Afiniki Thomas hari sun masa rauni mai muni a goshinsa. “An kama daya daga cikin maharan Sani Safiyanu domin bincike.

An garzaya da wanda aka yi wa raunin zuwa asibiti don yi masa magani.

“Kazalika, Dakarun na Safe Haven yayin sintiri sun tsinci gawar wani Paul Simon, mazaunin kauyen Yagbak a karamar hukumar Zangon Kataf.

An bada sanarwar bacewar mammacin a ranar 24 ga watan Maris, 2021. An birne gawarsa,” sanarwar ta kara da cewa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here