‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 11 a Jahar Katsina

‘Yan bindiga sun kai mummunan hari kauyen Dan-Kumeji da ke karamar hukumar Kankara a jahar Katsina.

An tattaro cewa sun kashe mutane 11 tare da jikkata wasu shida a harin da suka kai da misalin karfe 11:30 na dare.

Zuwa yanzu ba a ji ta bakin rundunar ‘yan sandan jahar ba kan lamarin.

Rahotanni sun kawo cewa ‘yan bindiga sun harbe akalla mazauna kauyen Dan-Kumeji da ke karamar hukumar Kankara a jahar Katsina 11 har lahira.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa mutane shida da suka samu raunuka a harin suna karbar magani a asibiti a yanzu haka.

Wani mazaunin garin, Abdulmumini Sani, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho, ya ce maharan sun afka wa kauyen da misalin karfe 11:30 na dare inda suka fara harbi ba kakkautawa, jaridar Thisday ta kuma rawaito.

Ya ce:

“Lokacin da mutanenmu suka gan su, sai suka fara gudu don tsira, ba tare da sanin cewa wasu daga cikin maharan sun yi kwanton bauna a wurare masu mahimmanci ba.Sai kawai suka fito suka fara harbin wadanda ke kokarin tserewa daga harin.”

Ya kara da cewa a safiyar yau Juma’a an kirga gawarwaki kusan 11 kuma ana ci gaba da shirye-shiryen binne gawarwakin da aka gano.

Kakakin ‘yan sanda a Katsina, SP Gambo Isah, bai tabatar da faruwar lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here