Shugaban ‘Yan Sintiri: ‘Yan bindiga sun kashe shi Tare da Garkuwa da Wasu a Jahar Katsina

 

Yan bindiga sun hallaka shugaban ‘yan sintiti na garin Maigora da ke karamar hukumar Faskari a Katsina.

Mallam Ummaru Balli ya riga mu gidan gaskiya ne sakamakon musayar wuta da suka yi da ‘yan bindiga a Rimi.

Baya ga kashe shugaban ‘yan sintirin, yan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutane takwas da suka sace daga Rimi.

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a daren Lahadi sun kashe shugaban kungiyar ‘yan sintiri a garin Maigora a karamar hukumar Faskari ta Jihar Katsina, Malam Ummaru Balli.

Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutum takwas yayin harin da suka kai a kauyen Rimi da ke karamar hukumar Sabuwa ta Jihar Katsina.

An gano cewa Mallam Balli ya jagoranci wasu ‘yan sintiri zuwa Rimi domin su taka wa ‘yan bindigan da suka kai hari a Rimi birki a dare da abin ya faru kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mazauna garin sun bayyana cewa yan sintirin sun yi musayar wuta da ‘yan bindigan hakan ya yi sanadin rasuwar Mallam Balli.

Yan bindigan daga bisani sun tsere sun tafi daji da mutum takwas da suka yi garkuwa da su.

Tuni dai an yi wa Mallam Balli jana’iza bisa koyarwar addinin musulunci.

Kawo yanzu mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, bai riga ya yi tsokaci kan lamarin ba.

Kazalika, mai bawa gwamna Aminu Masari shawara kan tsaro, Mallam Ibrahim Katsina bai daga wayarsa ba kuma bai turo da amsar sakon kar ta kwana da aka aike masa ba a lokacin wallafa wannan labarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here