‘Yan Bindiga Sun Kona Ofishin Hukumar zaɓe a Jahar Abia

 

Wasu yan bindiga sun sake kai hari ofishin hukumar zaɓe dake ƙaramar hukumar Ohafia a jahar Abia, inda suka cinna masa wuta.

Rahotanni sun nuna cewa babu wanda ya rasa ransa ko yaji rauni a yayin harin amma an lalata ginin ofishin tare da ƙone kayayyakin dake ciki.

A makon da ya gabata ne aka kai makamancin irin wannan harin a ofishin INEC ɗin dake ƙaramar hukumar Essien Udim a jahar Akwa Ibom.

A ranar Lahadi 9 ga watan Mayu, wasu yan bindiga suka cinna wuta a ofishin hukumar zaɓe dake Ƙaramar hukumar Ohafia jahar Abia.

A jawabin kwamishinan yaɗa labarai na INEC yace kwanan nan aka gyara ofishin da mutanen suka ƙona. Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da INEC ta fitar a shafinta na kafar sada zumunta wato Tuwita.

A jawabin dake jikin takardar, INEC tace wannan ba shine karo na farko da aka kaiwa ofishin hukumar hari a jihar ba.

Jawabin yace:

“Hukumar INEC tayi zama yau 10 g watan Mayu, ta kuma tattauna akan abubuwa da dama waɗanda suka haɗa da rahoto mara daɗi daga jahar Abia.”

“Kwamishin zaɓen jahar ya kawo rahoton cewa yan bindiga sun sake ƙona ofishin da hukumar ta gyara a baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Ohafia.”

“Lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi 9 ga watan Mayu, 2021, babu wani rahoton rasa rai ko jin rauni daga ɓangaren ma’aikatan mu da kuma masu gadi amma ginin wajen ya ruguje, sannan kuma duk wasu kayayyakin mu dake ciki sun ƙone.”

“Amma an miƙa rahoton duk abinda ya faru ga hukumar yan sanda domin su gudanar da Bincike.”

Idan baku manta ba a makon da ya gabata INEC ta samu rahoton kai hari a ofishinta dake karamar hukumar Essien Udim a jahar Akwa Ibom. INEC ta nuna matuƙar damuwarta kan hare-haren da ake kaiwa ofisoshinta wanda hakan ka iya jawo koma baya ga ayyukanta waɗanda suka haɗa da; cigaba da rijistar cancantar kaɗa ƙuri’a, gyara da kuma ƙara runfunan zaɓe, Zaɓen cike gurbi da kuma babban zaɓen 2023 dake tafe.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here