An Kuma: ‘Yan Bindiga Sun Sace Fasto a Jihar Kaduna
A sa’o’in farko na ranar Litinin, miyagun ‘yan bindiga sun sake yin garkuwa da wani fasto mai suna Rabaren fada Emmanuels Silas a Kauru ta jihar Kaduna.
Shugaban cocin katolika na Kafanchan, Rabaren Fada Emmanuel Uchechukwu Okolo ne ya sanar da hakan cike da takaici da kunar rai ga manema labarai.
A yayin kira ga al’umma da su kwanta da hankulansu tae da gujewa daukar doka a hannu, yace zasu bi duk wata halastacciyar hanya ta kubutar da faston.
Kauru, Kaduna – ‘Yan ta’adda a sa’o’in farko na ranar Litinin sun sake yin garkuwa da wani limamin cocin katolika, Rabaren Fada Emmanuel Silas a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
Shugaban Catholic Diocese ta Kafanchan, Rabaren Fada Emmanuel Uchechukwu Okolo, ya tabbatar da hakan a wata takardar da ga bai wa manema labarai a Kaduna, jaridar Leadership ta ruwaito.
Read Also:
Idan za a tuna, ‘yan ta’adda sun halaka Rabaren Fada Vaishima Barogo a gonarsa dake Kujama, kan babban titin Kaduna zuwa Kachia a ranar Alhamis, 25 ga watan Yunin 2022 kuma an birnes shi a ranar 30 ga watan Yunin 2022.
Shugaban cocin ya ce, “Cike da kunar rai muke sanar da garkuwa da aka yi da limaminmu, Rabaren Fada Emmanuel Silas. Lamarin ya auku a ranar 4 ga watan Yulin 2022 lokacin da muka fuskanci bai halarci bautar safe ba.
“An sace shi a iklisiya ta cocin katolika ta St. Charles dake Zambina a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
“Muna barar tsananin addu’ar saurin fitowarsa cikin koshin lafiya. Muna kira ga kowa da kowa da a kiyaye daukar doka a hannu. “Za mu yi amfani da duk wata halastacciyar hanyar wurin tabbatar da san sako shi lafiya cikin gaggawa.
“Muna fatan yesu da ya sadaukar da rayuwarsa, zai saurari addu’o’inmu tare da tabbatar gaggawar sakin limaminmu da sauran wadanda aka yi garkuwa da su.”