‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam’iyyar APC na Jahar Neja

Wasu yan bindiga sun sace shugaban jam’iyyar APC mai mulki na wata shiyya a jahar Neja ranar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa ɓarayin sun sace Aminu Bobi, shugaban APC na shiyyar C a gonarsa.

Wata majiya ta kusa da wanda aka sace ta bayyana cewa Bobi kaɗai ɓarayin suka sace yayin da masu aiki a gonarsa suka tsira.

Niger – Yan bindiga sun sace shugaban jam’iyyar APC na shiyyar C, Aminu Bobi, a yankin karamar hukumar Mariga, jahar Neja, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace Bobi ne yayin da ya je gonarsa domin sanya ido ga masu masa aiki ranar Asabar da yamma.

Wata majiya dake kusa da wanda aka sace ya bayyana cewa maharan sun farmaki gonarne a kan mashina shida, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Mutumin ya kara da cewa kowane babur yana ɗauke da mutum uku, inda suna zuwa suka buɗe wuta kan mai uwa da wani.

Mutumin tace:

“Maharan sun kai hari gonar a kan babura shida, kowane babur yana ɗauke da mutum uku. Da isar su suka buɗe wuta domin tsorata waɗanda ke wurin.”

Mutum nawa yan bindigan suka sace a harin?

Mutumin ya tabbatar da cewa Shugaban APC kaɗai yan bindigan suka yi awon gaba da yayin da ma’aikatan dake aiki a gonar suka tsira.

Duk wani kokarin tabbatar da lamarin daga rundunar yan sandan jahar Neja ya ci tura domin ba’a samu kakakin yan sandan Neja, DSP Wasiu Abiodun, ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here