‘Yan Bindiga Sun Saki ‘Dan Uwan Sakataren Gwamnatin Jahar Katsina

 

Gwamnatin Katsina ta saki mahaifin shugaban yan bindiga don su saki yayan sakataren jahar.

Yan bindigan sun sace yayan sakataren ne kimanin mako daya da ya gabata.

Gwamnatin jahar ta kafa sabbin dokokin kawo karshen matsalar tsaro.

Katsina- Kabir Muhammad, Yayan sakataren gwamnatin jahar Katsina, Muhammad Inuwa, da aka sace ranar Larabar da ta gabata, ya samu yanci bayan kwanaki shida.

Mai magana da yawun Inuwa, Kabir Yar’adua, ya tabbatar da hakan ranar Talata, rahoton Punch.

Yace:

“Lallai an saki dattijon amma babu kudin da aka biya na fansa.”

An samu labarin cewa an saki dattijon ne bayan damke wasu masu kaiwa yan bindiga bayanai a jahar, cikinsu har da mahaifin shugaban yan bindigan.

Majiyoyi sun bayyana cewa an tuntubi yan bindigan cewa an damke mahaifin shugabansu, sai yan bindigan suka yarda a sake yayan SSG Inuwa.

Wata majiya ta bayyana cewa, “Yan bindigan sun saki Yaya Muhammad da daren Litinin kuma ya koma wajen iyalansa.”

“Ba’a biya kudin fansa ba, saboda mun saki mahaifin shugaban yan bindigan a maimako bayan sun saki namu.”

Kakakin hukumar yan sandan jahar dai, SP Gambo Isah, bai tabbatar da labarin ba tukun.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here