‘Yan Bindiga Sun Shiga Ofishin ‘Yan Sanda Sun Tattara Makamai a Jahar Anambra

 

Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun afkawa wani sabon ofishin ‘yan sanda a Jahar Anambra.

Majiya ta bayyama cewa, an yi harbe-harbe tsakanin ‘yan bindigan da ‘yan sandan ofishin.

An kuma ruwaito cewa, sun tattara wasu makamai da dama daga ofishin na ‘yan sanda.

Anambra – Wasu ‘yan bindiga a cikin motoci bakwai sun afkawa sabon ofishin ‘yan sanda na yankin Nnewi inda suka yi awon gaba da makamai.

A cewar wata majiya, ‘yan bindigar sun shigo sun yi harbe-harbe na sama da awa daya.

Harbe-harbe tsakanin ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba da ‘yan sanda a rundunar ‘yan sandan Nnewi a ranar Litinin 9 ga watan Agusta da yamma ya haifar da tashin hankali tsakanin mazauna yankin.

Daily Trust ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun shigo kusan motoci bakwai zuwa ofishin ‘yan sanda kuma sun fara harbi wanda ya dauki sama da awa daya.

Wani ganau wanda ba zai so a ambaci sunansa a rubuce ba ya ce ‘yan bindigar sun yi nasara kan ‘yan sanda inda suka yi awon gaba da makamai.

A cewar majiyar, a lokacin da aka samu karin karfin gwiwa daga rundunar sojojin ruwa, maharan sun tafi duk da an tattara cewa an bi su.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya ce ofishinsa bai samu wani rahoto kan lamarin ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here