‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 13, Sun Kona Ofishin ‘Yan Sanda a Jahar Neja
‘Yan bindiga sun kone ofishin ‘yan sandan garin Beri a jahar Neja, sun halaka rayuka 13.
Hukumar NEMA ta tabbatar da aukuwar harin inda tace jami’in dan sanda 1 ya rasu.
An sake da tabbatar da cewa wasu mazauna yankin sun tsira da miyagun raunika.
‘Yan bindiga sun kai mummunan hari garin Beri dake yankin Bobi na jahar Neja inda suka kona ofishin ‘yan sanda tare da sheke sama da mutane 13 da suka hada da jami’in dan sanda.
Hukumar NEMA ce ta tabbatar da harin a wata takarda da ta fitar a ranar Litinin wacce ta zo kasa da sa’o’i 24 da garkuwa da yaran Islamiyya a jahar.
Read Also:
Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, hukumar taimakon gaggawan tace wannan harin ya bar wasu jama’a da miyagun raunika. ‘Yan bindigan sun kara da kai hari Unguwan Malam Bako dake yankin Kotonkoro kuma sun sace mutanen da har yanzu ba a san yawansu ba.
Hukumar ta lissafo sunan mamatan kamar haka: Idris Ahmed Kwata, Hadiza Umaru Tunga, Momi Dalladi, Ibrahim Dalkadi, Yau Dalladi, Saadiya Garba, Garba Umar Tashanjirgi, Hussaini Shuaib, Ayuba Garba, Abdullahi Jodi, Alhaji Isah Kasakohi da Fatima Nasiru Kwata.
Jahar Neja ta fi kowacce jaha girma a kasar nan kuma tana daga cikin jahohin da miyagun al’amuran ‘yan bindiga suka fi kamari a kasar nan.
A wata takarda da gwamnan jahar, Abubakar Bello, ya fitar a ranar Lahadi, ya kwatanta halin tsaron da jahar ke ciki da na yaki.
“Halin da ake ciki yanzu ya kai na rikici, a takaice zamu iya cewa yaki ne dole mu tunkare shi babu tsayawa,” yace.