‘Yan Bindiga Sun Harbe ɗalibin Jami’ar Jahar Ribas

 

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun harbe ɗalibin jami’ar jahar Ribas har lahira da safiyar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama wani ɗalibi ɗan aji 2 da hannu a lamarin kisan.

Hukumar yan sanda ta tabbatar da kisan ɗalibin, tace yanzun haka kan bincike don kamo yan bindigan.

Rivers – An shiga yanayin tashin hankali a jami’ar jahar Ribas (RSU) yayin da wasu yan bindiga suka harbe ɗalibin makarantar har lahira, kamar yadda vanguard ta rawaito.

Dalibin da aka kashe, wanda har yanzun ba’a gano asalin sunanshi ba, an tabbatar da yana karatun injiniya ne a jami’ar.

Rahotanni sun bayyana cewa an harbe ɗalibin ne a haraban ginin tsangayar kimiyya, inda ya fita shakatawa da abokansa.

Su wa ake zargi da aikata kisan?

Wata majiya da ya bayyana sunansa da Emmanuel, yace ana zargin ɗalibin aji 2 da hannu a kisan mamacin.

Emmanuel yace an harbi dalibin ne a tsakiyar kansa, kuma lamarin ya faru da misalin karfe 9:00 na safiyar Alhamis.

Ya kara da cewa makasan ɗalibin sun tsere daga wurin kafin daga bisani jami’an tsaro suka cafke ɗalibin aji 2 da zargin yana da hannu a lamarin.

Wane mataki jami’an tsaro suka ɗauka? Kakakin rundunar yan sanda reshen jahar Ribas, SP Nnamdi Omoni, ya tabbatar da faruwar lamarin da safiyar ranar Alhamis.

Omoni yace:

“Ina tabbatar da faruwar lamarin a jami’ar jahar Ribas da safiyar nan. Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin sun aikata kisan ya shiga hannu.”

“Kwamishinan yan sanda ya kaddamar da binciken kamo waɗanda suka aikata kisan kuma ba da jimawa ba zasu shiga hannu.”

“A halin yanzun an samu kwanciyar hankali a jami’ar, mun dawo da zaman lafiya a cikin makarantar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here