Bincike ya Nuna  Cewa ‘Yan Boko Haram ke Horar da Makiyaya Dabarun Yaki

 

Sabon bincike ya nuna cewa ‘yan ta’addan Boko Haram suna horar da makiyaya dabarun yaki.

An gano cewa ‘yan ta’addan basu bar makiyayan ba, suna karbar harajin sa daya a cikin kowanne shanu 40.

Majiyar ta tabbatar da cewa wannan ya zama ruwan dare a wasu kauyukan Gonisaleri, Dawayya da Abari a Geidam.

Kamar yadda SaharaReporters ta wallafa, makiyaya da ‘yan Boko Haram sun kulla wata yarjejeniya mai tsari a wasu yankuna na jahar Yobe inda ‘yan Boko Haram ke horar da makiyaya dabarun yaki.

SaharaReporters ta tabbatar da cewa wata majiya daga rundunar sojin Najeriya tace ‘yan ta’addan na karbar sa daya a kowanne shanu 40 da sauran kayan abinci daga makiyayan a matsayin haraji.

An gano cewa, wasu daga cikin makiyayan da suka hada da kananan yara, ana basu makamai tare da horar dasu ta yadda za su gudanar da hari na gaba.

“Horar da makiyaya da karbar haraji daga wurinsu ba yau aka fara ba a garin Geidam dake jahar Yobe.

‘Yan ta’addan na bukatar abinci da suka hada da nama kuma suna horar da makiyaya a kauyukan Gonisaleri, Dawayya da Abari duk a karamar hukumar Geidam,” majiya daga rundunar soji ta sanar. ”

‘Yan ta’addan na karbar sa daya a duk shanu 40 a matsayin haraji, suna bada hatimi tare da shaidar biya ga makiyaya. Abun tamkar a shirye ake yinsa,” ya sake bayyanawa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here