Kungiyar ‘Yan China Mazauna Najeriya Sun yi Alla-Wadai da Kashe Ummita

 

Kungiyar Sinawa ‘yan kasuwa a Najeriya ta yi alla-wadai da kisan da ake zargin wani mambanta, Geng Quanrong ya yi wa matashiya Ummukhulthum Sani Buhari a Kano.

Da take mika sakon ta’aziyya ga iyayen Ummulkhairi wadda aka fi sani da suna Ummita, kungiyar ta ce tana ba da cikakken goyon baya ga doka ta yi aikin ta.

A cikin sanarwar da ta fitar kungiyar ta ce abin da ake zargin Geng Quanrong ya aikata, abin alla-wadai ne kuma babban laifi ne da ya kamata a bar hukumomin tsaro su yi aiki don tabbatar da abin da ya faru.

Tuni dai Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce zai tabbatar da ganin shari’a ta yi aikinta a kan batun kisan na Ummita.

Ranar Juma’a da dare ne, Geng Quanrong dan shekara 47 ya kutsa kai gidansu Ummita a unguwar Kabuga cikin karamar hukumar Gwale.

Mahaifiyar Ummita, Hajiya Lami Sani Buhari ta ce Mista Geng ya bangaje ta, sannan ya kutsa kai cikin dakin Ummita, kuma da ganin ta sai ya zare wuka ya yi ta caka mata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here