Ƴan Fashi sun Kashe Sojojin Nijar 5

Rahotanni na cewa sojojin Jamhuriyar Nijar guda biyar ne suka rasa ransu a jihar Agadez yayin da suke yi wa ayarin masu haƙar zinare rakiya.

Wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba ne suka kai wa ayarin harin, sannan suka yi awon-gaba da zinaren.

Shugaban karamar hukumar Arlit, Noura Mallam Sani ya tabbatar wa BBC cewar akwai wasu sojojin da suka samu raunuka baya ga waɗanda suka rasa rayukan nasu.

Matsalar masu fashi da makami a kan masu haƙar zinare a ƙasar ta Jamhuriyar Nijar dai ta daɗe tana ci wa al’umma tuwo a ƙwarya.

Sai dai hukumomin ƙasar na cewa suna bakin ƙoƙarin su wajen shawo kanta.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here