Har Yanzu Bamu Kai ga Yanke Shawara Kan Kristalina Georgieva – IMF
Asusun ba da Lamuni na Duniya ya ce har yanzu bai kai ga yanke shawara kan daraktarsa, da ake ta takaddama a kanta ba.
IMF ya ce ya tattauna da Kristalina Georgieva a karshen mako, kuma ana samun gagarumin ci gaba wajen gano gaskiya.
Binciken wani kamfanin shari’a mai suna WilmerHale ya yi zargin cewa, yayin da a baya ta ke aiki a Bankin Duniya, matar ta rika matsa ma’aikatan da ke wurin lamba don fifita China.
Ta shaida wa hukumar zartarwa ta IMF cewa zargin ya samo asali ne daga kunji-kunji.
Ana sa ran batun zai mamaye taron shekara -shekara na asusun na IMF da Bankin Duniya, wanda za a fara yau.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here