‘Yan kwallon Najeriya da Zasu kara da Sierra Leone
Yayinda ake saura kwanaki uku wasan kwallon fidda gwanin gasar kofin nahiyar Afrika wanda akafi sani da AFCON.
tsakanin Najeriya da Sierra Leone, gwarazan yan wasan Super Eagles sun dira jihar Edo.
Yan kwallon a yau sun motsa jiki a filin kwallon San Ogbemudia dake birnin Benin tare da mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu.
Daga cikin yan wasan da suka hallara a cewar NFF sune:
Ahmed Musa
William Troost-Ekong
Alex Iwobi
Ola Aina
Joe Aribo
Leon Balogun
Kevin Akpoguma
Sebastin Osigwe
Zaidu Sanusi
Tyronne Ebuehi
Read Also:
Etebo Oghenekaro
Maduka Okoye
Ikechukwu Ezenwa
Chidozie Awaziem
Kelechi Iheanacho
Emmanuel Dennis
Wanna itace wasa ta farko da yan kwallon Najeriya zasu buga domin samun gurbin shiga sahun kasashen da zasu kara a gasar Afcon 2022.
Za’a buga wasanni biyu tsakanin dukkan kasashe; daya a gida, daya a waje.
A wasar farko, Najeriya zata karbi bakuncin yan kwallon kasar Sierra Leone a filin kwallon Samuel Ogbemudia dake birnin Benin, jihar Edo.
Za’a buga wasar ranar Juma’a, 13 ga watan Nuwamba, 2020.
Bayan haka yan kwallon Najeriya zasu garzaya filin kwallon Siaka Stevens dake Freetown, kasar Sierra Leone ranar 17 ga Nuwamba, 2020.