‘Yan Majalisar Wakilai Sun Koka Kan Azababben Zafin da ke Majalisar 
‘Yan majalisar wakilai a ranar Talata sun koka akan azabar zafin da ya barke mu su a majalisar.
 Dan majalisar, Haruna Dederi ya bukaci a yi duba kuma ayi gaggawar gyara musu na’urar sanyaya wuri ta AC.
Kamar yadda ya yi korafi, ko dai su hakura da zaman majalisa a yau ko kuma a yi gaggawar gyara musu AC din.
Abuja – Majalisar wakilai na Tarayya a ranar Talata ta yi gaggawar datse zamanta sakamakon korafin da ‘yan majalisar su ka dinga yi akan azababben zafin da ke majalisar.
 Wani dan majalisar, Haruna Dederi, dan jam’iyyar APC daga Kano, ya bukaci a dage zaman majalisar.
Yayin da yake daga maganar, kamar yadda Vanguard ta rawaito, ya ce:
 “Ranka ya dade, doka ta 7 ta gidannan ta ba mu damar samun cikakken iko dangane da samun natsuwa yayin zama a majalisar nan.”
 “A samar mana da cikakkiyar natsuwa wurin yin ayyukan da su ka dace. Saboda a halin yanzu muna wahala sakamakon azababben zafin da majalisar nan take da shi.
 “A tawa shawarar, ya kamata a dage mana zaman yau ko kuma a yi gaggawar gyara na’urar sanyaya wuri ta AC dake majalisar nan.
 “Duk yadda za ayi, a yi kokarin yi don samar mana da natsuwa a cikin majalisar nan”.
Kakakin majalisar ya ce abin duba wa ne
Yayin da kakakin majalisa ya yi nazari akan maganar ta Dederi, bisa ruwayar Vanguard cewa ya yi:
 “Wannan maganar gaskiya ce, kuma yanzu mu ka gama tattaunawa da mataimaki na a kai.
 “Ina ganin abinda za ayi shi ne kowa ya tafi ya yi sallah, in ya so sai mu sanya wannan batun a matsayin mahawara don samun hanyar da za a bullo wa lamarin da sauri.
“Mun dauki wannan batu kuma kowa zai iya yin tafiya.”
Ranar Talata ce rana ta biyu da majalisar ta tayar da zaman ta sakamakon yadda ‘yan majalisar su ke a takure yayin zama a majalisar.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here