‘Yan Najeriya Sun Nuna Rashin Jindadinsu Kan Karin Kudin Wutar Lantarki

 

‘Yan Najeriya sun bayyana rashin jin dadinsu dangane karin kudin wutan lantarki a kasar.

Sun bayyana cewa gwamnati da hukumar wutan lantarki sun yaudari ‘yan Najeriya kan karin.

Hakazalika sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da halin da ake ciki na tsadar kudin wutan lantarki.

‘Yan Najeriya na ci gaba da gunaguni kan karin wuce gona da iri na kudin wutar lantarki da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya ta aiwatar.

NERC, wacce ta amince da karin kudin da kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) ta fitar, ta ce karin ya kasance tsakanin N2 zuwa N4, amma wani bangare na masu amfani da wutar da suka sake cajin mitocin su kwanan nan, sun nace cewa karin ya haura N4.

Aminiya ta tattauna da ’yan Najeriya don gano yadda hawan ya shafi amfani da wutar lantarki da suke yi.

Jimillar mutane 494 suka halarci zaɓen kuma kashi 45.3 cikin ɗari sun bayyana cewa suna biyan ninki biyu na abin da suke biya kafin karin.

Kusan kashi 36.4 sun lura cewa harajin ya ninka sau uku yayin da kashi 11.3 ya bayyana cewa kawai sun ɗan sami ƙari ne.

Kuma kashi 6.9 na wadanda suka amsa sun ce jadawalin karin kudin ya kasance kamar yadda yake.

Wani mai amfani da shafin Twitter, @BigMikeforyou ya bayyana cewa

“karin kudin wutar lantarki ya rubanya idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata. A da mun samu kusan adadin yunit 80 a N2,000 amma yanzu 45 muke samu a N2,000. Yanzu mun daina amfani da dutsen guga da sauran kayan lantarki da ke cin wutar lantarki da yawa.

” A wani rahoto da Aminiya ta gabatar a baya, wani mai amfani da shafin Twitter, Richard Daniel a karkashin Port Harcourt DisCo, ya ce galibi ya kan samu yunit 153.9 idan ya sayi na N5000. Don da haka, wannan ya ragu zuwa yunit 88 a yanzu, yana nuna kashi 42 cikin ɗari.

Shamsudeen Ibrahim, wani mazaunin Abuja ne a karkashin Abuja DisCo, ya ce a baya, yunit na N10,000 yakan kai yunit 386 ya zuwa watan Nuwamba amma ya samu 197 kwanan nan. “Wannan shi ne kusan kashi 49 cikin ɗari.

Ana yaudarar mu kawai cewa karin bai wuce N4 ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here