An Yankewa Wasu ‘Yan Najeriya Hukunci Mai Zafi a UAE

Wato kotun kasar hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta zartar da hukunci a kan wasu ‘yan Najeriya shidda.

Ana zargin mutanen da yin amfani da kudadensu wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram.

Biyu daga cikinsu an yanke musu hukuncin daurin rai da rai a gidan yari, sauran hudun kuma daurin shekara goma Wata kotun tarayya a Abu Dhabi Dubai, ta yankewa ƴan Najeriya shidda hukunci bisa zarginsu da ɗaukar nauyin Boko Haram, kamar yadda binciken jaridar Daily Trust ya gano kuma ya wallafa.

Biyu daga cikin waɗanda ake zargin, Surajo Abubakar Muhammad da Saleh Yusuf an yanke musu hukuncin zaman gidan yari iya tsawon rayuwarsu.

Su kuwa sauran mutane huɗun da suka haɗar da; Ibrahim Ali Alhassan, AbdurRahman Ado Musa, Bashir Ali Yusuf, da Muhammad Ibrahim Isa, dukkansu an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara goma.

Waɗanda ake zargin,acewar tuhumar Kotun da jaridar Daily trust ta gano,ana tuhumar masu laifin tun shekarar 2019.

Kotun ta gano cewar daga shekarar 2015 zuwa 2016, waɗanda ake zargin sun tura zunzurutun kuɗaɗe har Dala $782,000 zuwa ƙungiyar Boko Haram, sai dai makusantan wadanda ake zargin sun ce an tura kuɗin ne a bisa halal ba don daukan nauyin ayyukan ta’addanci ba.

Sama da shekaru 11 da suka gabata, ana fama da ruɗani gami da sarƙaƙiya akan masu d’aukar nauyin k’ungiyar.

Wannan shine kusan karo na farko da aka gano masu aikata hakan a wajen Najeriya.

Wani babba daga jami’i a cikin gwamnatin Najeriya yace sun san da kwanan zancen.

Har yanzu gwamnatin tarayya ba ta sanar da sunaye balle ta zartar da hukunci a kan ma su daukar nauyin kungiyar Boko haram ba duk da rundunar soji ta sha ikirarin cewa sun san ma su yin hakan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here