Jami’an ‘Yan Sanda 21 Sun Rasa Rayukansu a Harin da ‘Yan Bindiga Suka Kai Jahar Akwa Ibom

 

Hukumar yan sanda a jahar Akwa Ibom ta bayyana wa gwamnan jahar cewa jami’an yan sanda 21 ne suka rasa rayukansu a harin da yan bindiga suka kai musu a jahar.

Kwamishinan yan sandan jahar, Amiengheme Andrew, shine ya bayyana wa gwamnan a wata ziyara da ya kai hedkwatar su domin yin ta’aziyya.

Gwamnan ya sanar da bayar da kyautar kuɗi 60 miliyan ga iyalan gwarazan yan sandan da suka rigamu gidan gaskiya a wajen ƙoƙarin tsare jahar Hukumar yan sanda a jahar.

Akwa Ibom ta bayyana cewa jami’an yan sanda 21 ne yan bindiga suka hallaka a hari daban-daban da suka kai faɗin jahar.

Kwamishinan yan sandan jahar, Amiengheme Andrew, shine ya bayyana haka a ranar Litinin yayin da yake jawabi ga gwamnan jahar, Udom Emmanuel, a hedkwatar yan sanda, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Gwamna Udom Emmanuel, ya kai ziyara hedkwatar yan sandan ne domin yayi ta’aziyya ga iyalan gwarazan yan sandan da suka rasa rayukansu.

Kwamishinan yace:

“Jami’an mu 21 ne suka riga mu gidan gaskiya sanadiyyar harin da yan bindiga suka kai musu a lokaci daban-daban.”

“Hakanan kuma motocin mu 11 sun salwanta a yayin hare-haren, sannan mun rasa bindigogi 7.”

“Nayi matuƙar farin ciki da wannan ziyara, kuma munyi alƙawarin cewa hukumar mu zata cigaba da yin iyakar bakin ƙoƙarinta wajen kare jahar daga dukkan matsalolin tsaron da take fama dasu.”

A yayin wannan ziyarar, gwamnan ya sanar da bada tallafin kuɗi 60 miliyan ga iyalan yan sandan da suka rasa rayuwarsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here