Yan Sanda 4 Sun Rasa Rayukansu Sanadiyyar Artabu Tsakaninsu da ‘Yan Bindiga a Jahar Anambra

 

Rahotanni sun ce an kashe jami’an ‘yan sanda hudu a wani artabu tsakanin ‘yan sanda da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba.

Wasu da ake zargin yan asalin yankin Biafra (IPOB) ne suka kai aiwatar da harin wanda ya faru a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, a ofishin ‘yan sanda da ke Nnewi, jahar Anambra.

Daraktan yada labarai na IPOB, Emma Powerful ya ce za a takaita zirga -zirgar mutane da ababen hawa a duk fadin kasar Biyafara duk ranar Litinin, har sai an sallami jagoran nasu ba tare da wani sharadi ba.

Anambra- Harin da ake zargin wasu ‘yan asalin Biafra (IPOB) ne suka kai ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an’ yan sanda hudu.

Harin wanda ya faru a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, ya kasance ne sakamakon artabun da ya barke tsakanin ‘yan sanda da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba a ofishin ‘yan sanda da ke Nnewi, jahar Anambra.

A wata hira da gidan talabijin na Channels TV, kakakin rundunar ‘yan sandan jahar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya ce har yanzu ofishinsa bai samu cikakken rahoto kan lamarin ba.

Ya kara da cewa ‘yan sanda sun yi fafatawa da maharan. Majiyoyi sun sanar da cewa, ‘yan bindigar sun kai farmaki kan rundunar ‘yan sanda a ranar Litinin da rana kuma suka yi artabu da jami’an tsaron.

An shafe sama da sa’a guda ana arangama da maharan wadanda suka zo kai farmaki ofishin ‘yan sanda a cikin motoci bakwai, Channels TV ta nuna.

Wannan harin ya kara haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin yayin da suka tsere don samun mafaka duk da cewa sojojin sun bi bayan maharan ba tare da samun nasara ba.

Kungiyar ta bakin Daraktan yada labaranta, Emma Powerful ta ce za a takaita zirga -zirgar mutane da ababen hawa a duk fadin kasar Biyafara duk ranar Litinin, daga jiya, 9 ga watan Agusta, har sai an sako Nnamdi Kanu ba tare da wani sharadi ba, Vanguard ta ruwaito.

Hakazalika,ana zaton cewa harin ramuwar gayya ce daga kungiyar da aka haramta bayan kashe wasu membobin su biyu a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here