‘Yan Sanda Jahar Osun Sun Aika ‘Yan Bindiga 3 Lahira

Rudunar ‘yan sandar jahar Osun ta ce ta sheke mutane 3 ya yin musayar wutar da ta shiga tsakaninsu a jahar.

Dama wadanda ake zargin sun kai wa motar ‘yan sandan farmaki kamar yadda ‘yan sandan suka tabbatar.

Lamarin ya faru a titin Osogbo-Ilesa bayan rafin Osunjela a ranar 25 ga watan Augustan 2021 da misalin 3:30pm.

Osun – Hukumar ‘yan sanda na jahar Osun ta ce sun samu nasarar sheke wasu da ake zargin makasa ne yayin musayar wutar da ta auku tsakaninsu bayan sun kai wa motar ‘yan sandan farmaki.

TheCable ta rawaito cewa, kamar yadda ‘yan sandan suka tabbatar, an kai wa abin hawansu hari ne a ranar Laraba a kan titin Osogbo zuwa Ilesa bayan rafin Osunjela.

‘Yan sandan sun ce suna tafe da wadanda ake zargin ne daidai Ilesa domin mika su gidan gyara hali amma sai motarsu ta lalace.

Ana tsaka da gyaran ne sai ga wasu ‘yan bindiga guda 4 a babura suka kai musu farmaki suna kokarin ceton wadanda ake zargin makasan ne, TheCable ta rawaito.

Harin wanda ya kai ga musayar wuta tsakanin ‘yan sanda da ‘yan bindiga, ya yi sanadiyyar ajalin mutane 3 daga cikin ‘yan bindigan.

Ranar 25 ga watan Augustan 2021 da misalin 3:30pm, ‘yan sanda suna tafe da wasu da ake zargin makasa ne za su kai su gidan gyaran halin Ilesa, bayan rafin Osunjela wuraren titin Osogbo da ke Ilesa, sai motar ta samu matsala, a cewar Opalola Yemisi, kakakin hukumar ‘yan sanda kamar yadda takardar ta zo.

Wasu kanikawa suna tsaka da gyaran motocin ne sai ga ‘yan bindiga 4 daga titin Osunjela a babura kirar Bajaj inda suka kai wa ‘yan sandan farmaki suna harbe-harbe.

Bayan sun sha ragargaza daga wurin ‘yan sandan suka tsere suka suka bar baburansu da bindigogin toka 3, adduna da sauran miyagun makamai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here