Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas na Ci gaba da Bincike Kan Mutuwar ‘Dan Mawaki Davido

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ce har yanzu tana rike da mai kula da Ifeanyi Adeleke dan mawaki Davido wanda ya nutse a wajen ninkaya a gidan mahaifinsa da ke Ikoyi.

Kakakin rundunar Benjamin Hundeyin ya shaidawa BBC cewa suna ci gaba da binciken abin da ya janyo mutuwar yaron mai shekaru uku a duniya.

A ranar Talata ne ‘yan sanda suka gayyaci ma’aikata takwas a gidan mawakin domin yi musu tambayoyi kan mutuwar yaron.

“Muna ci gaba da binciken kwa-kwaf game da lamarin da ya faru,” in ji Hundeyin.

Ifeanyi shi ne yaro ɗaya tilo da David Adeleke (Davido) ya haifa tare da budurwarsa Chioma Rowland.

A kwanakin baya ne dai Davido ya sanar da cewar zai auri mahaifiyar ɗan nasa Chioma Rowland a shekara mai zuwa (2023).

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here