Rundunar Ƴan Sandan Jihar Ƙatsina ta Cafƙe Gawurtaccen ɗan Bindiga
Rundunar ƴan sandan jihar Ƙatsina ta samu nasarar cafƙe wani gawurtaccen ɗan bindiga da ta daɗe tana nema.
Sai’du Yaro wanda yake da hannu wajen kisan kwamandan ƴan sandan yankim Dutsinma, ya shiga hannu ne bayan an dadr ana nemansa.
Ɗan bindigan ya amsa laiɗin haɗa baki da wasu ƴan bindigan wajen babban kwamandan ƴan sandan.
Jihar Katsina – Ƴan sanda sun cafke wani wani ɗan bindiga mai suna Sa’idu Yaro wanda aka fi sani da Sabon Jini mai shekar 30 a duniya, wanda ake zargin yana da hannu wajen kashe ACP Aminu Umar, Kwamandan ƴan sandan Dutsinma a jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun halaka ACP Umar ne a ranar 5 ga watan Yuli a wani kwanton ɓauna da suka yi masa lokacin da yake jagorantar tawagar sintiri a aikin da aka saba yi na fatattakar ‘yan ta’adda a yankin, cewar rahoton PM News.
Read Also:
Ƴan bindigan sun yi galaba akan ƴan sandan ne a ƙazamin artabun da suka yi wanda a ƙarshe aka halaka ACP Umar da wani jami’i.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, SP Aliyu Abubakar-Sadiq, ya gaya wamanema labarai a ranar Alhamis cewa, an kama wanda ake zargin, Sa’idu Yaro wanda aka fi sani da Sabon Jini a ranar 30 ga watan Agusta.
Wanda ake zargin ya fito ne daga ƙauyen Tsaskiya da ke ƙaramar hukumar Safana a jihar Katsina.
Yadda aka cafke ɗan bindigan A kalamansa: “Wanda ake zargin ya kasance cikin jerin sunayen da ƴan sanda da ke nema ruwa a jallo bisa wasu laifuka, kamar satar mutane, satar shanu da sauran munanan laifuka.”
“Dubunsa ta cika ne lokacin da aka kama shi da laifin yin garkuwa da wani Hussaini Nabara da ke ƙauyen Kagara a ƙaramar hukumar Dutsinma.”
“A yayin bincike, an gano cewa shi ɗan ƙungiyar wani Abubakar Jankare ne, wani fitaccen shugaban ƴan bindiga a yankin.”
Kakakin ƴan sandan ya kuma ƙara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifin haɗa baki da wasu miyagun ƴan bindiga domin yi wa marigayi ACP Umar kwanton ɓauna da halaka shi.