‘Yan Sanda Sun Ceto Jami’an INEC 19 da Akai Garkuwa da su a Safiyar Yau
Yan sanda sun kubutar da jami’an INEC 19 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Imo.
Wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace jami’an zaben na wucin gadi a hanyarsu ta zuwa mazabun da za su yi aiki.
Sai dai ba a yi nasarar kwato kayayyakin zabe da na’urorin BVAS daga maharan ba.
Imo – Jami’an rundunar yan sanda a jihar Imo sun ceto jami’an hukumar zabe na wucin gadi guda 19 da aka yi garkuwa da su a safiyar ranar Asabar a jihar.
Read Also:
Hukumomin INEC a jihar ne suka tabbatar da ci gaban kamar da gidan talbijin na Channels ta rahoto.
A cewar mahukunta, jami’an zaben 19 na a hanyarsu ta zuwa rumfunan zabensu mabanbanta a gudunmar Ugbelie 06 a karamar hukumar Ideato ta kudancin jihar Imo lokacin da aka yi garkuwa da su.
INEC ta tabbatar da ceto jami’anta 19 da sace a Imo Mai magana da yawun hukumar INEC, Chinenye Chijioke-Osuji, ya ce an ceto mutanen ne bayan wani kira mai cike da damuwa da kuma ba jami’an tsaron bayanai game da lamarin. Nan take sai suka shiga aiki.
Ta kara da cewar koda dai an ceto su, ba a samu damar kwato kayayyakin zaben da suka hada da BVAS da sauransu ba, rahoton Vanguard.