‘Yan Sanda Sun Ceto Mutane 4 Daga Maboyar ‘Yan Bindiga a Abuja

Yan sanda da mafarauta a Birnin Tarayya Abuja sun yi nasarar ceto wasu mutane hudu daga maboyar yan bindiga a ranar Laraba.

Jami’an tsaron sun kai samamen ne a Dutsen Dudu inda suka yi musayar wuta suka kuma fatattaki miyagun sannan suke lalata maboyar.

Mafarauci guda ya riga mu gidan gaskiya yayin samamen kuma rundunar yan sanda ta mika ta’aziyya ga iyalansa ta kuma yi alkawari cigaba da sauke nauyin da doka ta dora mata.

Abuja – Yan sanda a Abuja a safiyar ranar Laraba 1 ga watan Yunin 2022, sun ceto mutane hudu daga mabuyar masu garkuwa a Dutsen Dudu a unguwar Kuje sun kuma lalata maboyar yan ta’addan.

Rundunar yan sandan ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Sanarwar da ke tabbatar da samamen ta ce:

“Bayan samun bayannan sirri kan wasu yan bindiga da suka yi garkuwa da wasu mutane a Abuja, yan sanda tare da mafarauta sun tafi Dutsen Dadu ta karamar hukumar Kuje, suka ragargaji yan bindigan, suka lalata maboyarsu sannan suka ceto mutum hudu.

“Samamen da aka kai misalin karfe 6 na safiyar ranar Laraba 1 ga watan Yunin 2022 ya yi sanadin ceto Mustahudeen Sani, Felix Vaa da Adamu wadanda aka sace tsakanin ranar 23 zuwa 25 na watan Mayun 2022 a Kiyi da Abdulsalam Uzugiz da aka sace a Angwan Gade na karamar hukumar Kuje.

“Yayin da yan bindigan suka hangi jami’an tsaron sun yi musayar wuta da su inda wani mafarauci daya ya riga mu gidan gaskiya.

“Bata garin sun tsere da raunin bindiga saboda jami’an tsaron sun fi karfinsu. An kuma kai wadanda aka ceto asibiti don a duba su kafin a sada su da iyalansu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here