Yanda ‘Yan Sanda Suka Ci Mutuncin Wani Direba

An samu hayaniya tsakanin Direbobi da ‘yan sanda a garain fatakwal

Jami’an tsaron sun tube wani Direban mota, sun yi masa sintir kan titi.

Ana zargin an wulakanta wannan mutumi ne saboda kin bada rashawa.

Jaridar Punch ta rahoto cewa an yi hayaniya a yankin Ada George a garin Fatakwal, jihar Ribas, yayin da ‘yan sanda su ka ci mutuncin wani direba.

A ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, 2020, wasu gungun ‘yan sanda a Fatakwal, jihar Ribas su ka tare wani direba, su ka cire masa kayan jikinsa.

Wannan abin kunya ya wakana ne a lokacin da jami’an tsaron suka bukaci wannan mutumi mai suna Emenike ya basu cin hancin da su ke karba.

Rahoton ya ce wannan mutumi ya yi taurin-kai, ya ki ba ‘yan sandan cuwa-cuwa, sai su ka tsare shi, su ka tube shi da rana-tsaka, ana ji-ana gani.

sauran direbobi da ke aiki a wannan unguwa a Fatakwal da ke ribas sun yi bore domin nuna ba su ji dadin wannan abu da aka yi wa abokin aikinsu ba.

Wani shugaban kungiyar Direbobi na shiyyar Choba, Bestman Chile yace ‘yan sanda sun nemi cin hanci da rashawa ne inda Emenike ya ki ba su komai.

Wani wanda abin ya faru a gaban idanunsa ya ce: “Ya shiga motar Emenike, ya fada ya tuka zuwa wajen da ‘yan sanda su ke.”

“A hanyarsa, sai ‘dan sandan ya fara dukansa da sanda, shi kuma ya na kici-kici da shi da wannan mutumi da kan mota.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here